Ba zan yi jinkiri wajen rattafa hannu kan hukuncin kisa kan makashin Hanifa ba, inji Ganduje


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ba zai bata lokaci wajen rattafa hannu kan hukuncin kisa kan Abdulmalik Tanko ba idan kotu tayi hakan
.

Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayinda ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyayen Hanifa Abubakar a gidansu dake Dakata/Kawaji.

Gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa, Dr Nasiru Gawuna; shugaban masu rinjaye a majalisar jihar, Labaran Abdul Madari; da wasu manyan jiga-jigan gwamnati.

Yace:

"Mun samu labarin cewa kotu zata tabbatar da anyi adalci. Duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci kisa ba tare da bata lokaci ba."

"Kundin tsarin mulkinmu ya bukaci cewa idan an yanke hukuncin kisa, gwamna na da karfin rattafa hannu a kashe mai laifi. Ina tabbatar muku cewa ba zan bata lokaci ko dakika guda ba."

"Gwamnati zata kula da iyalan 'yarmu marigayiya Hanifa."

A cewarsa, za a kafa wani kwamiti na musamman wanda zai tantance makarantu kuma za ta fitar da wasu matakai da za a yi amfani da su wurin tantance makarantun kudi a jihar.

Hakazalika, ya ce dukkan makarantun masu zaman kansu da ba su cika sharuddan da za a gindaya musu ba, sun tafi kenan, ma'ana ba za a bude su ba.

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN