Sanatan da ake tuhuma bai da laifi, ‘Yan Sanda sun jefi masu zarginsa da laifi


An gano cewa Sanatan da ake zargi da laifin lalata da matar aure, bai aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba, sharrin ‘yan siyasa ne kurum.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a ranar 20 ga watan Junairu 2022 da ya bayyana cewa an gano gaskiyar abin da ya faru da Sanata Godiya Akwashiki.

Jami’an ‘yan sanda suka bayyana wannan bayan jaridar sun bukaci sakamakon binciken da suka yi.Akwashiki ya tabbatar da hakan da aka nemi jin ta bakinsa.

A lokacin da abin ya faru Godiya Akwashiki ya na kan kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawan jihar Nasarawa, kuma ya lashe zaben Sanata kenan.

Zargin da aka jefi Akwashiki da aikatawa

An zargi Sanata Akwashiki da laifin neman matar wani ‘dan siyasa daga jiharsa ta Nasarawa, Danladi Envulanza, wanda hakan ya sa aka ci masa mutunci.

Da bidiyo ya bayyana aka ga ‘dan majalisar na Nasarawa ta Arewa yana neman Amina Danladi Halilu a gidan mijinta, sai ‘yan iskan gari suka yi masa la-las.

A farkon watan Maris a 2019, Amina Halilu ta shigar da karar Akwashiki wajen rundunar ‘yan sanda da ke Maitama a Abuja, ta ce ya nemi ya yi lalata da ita.

Ya aka ji shiru?

Ganin an dauki lokaci ba a sake jin labarin inda aka kwana a wannan kara ba, sai 'yan jaridar suka tuntubi rundunar ‘yan sanda domin jin inda aka kwana.

Wani jami’in ‘yan sanda a garin Abuja, Fom Pam Joseph a madadin kwamishinan da ke binciken masu manyan laifuffuka ya fadawa jaridar sakamakon bincikensu.

Sanata bai da laifi

A cewar Fom Pam Joseph, Misis Envulanza ba ta iya tabbatar da ikirarin da ta ke yi ba, sai dai ma aka samu mai gidanta da bata suna da aikata wasu laifuffukan.

‘Yan sanda sun samu Danladi Halilu Envulanza “m”, Jamilu Halilu “m” Abdullahi Aliyu Ogah “m”.” da aikara laiffukan da suka sabawa wasu sassa na dokar final kwad.

A cewar jami’an tsaro, ‘yan siyasan biyu sun jaye karar da aka kai a kotu, sun sasanta tsakaninsu.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN