Tsohon dan takarar shugaban kasa ya fice a APC, zai nemi tikiti a tsagin adawa


Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin SDP, kuma jigon APC, Chief Reuben Famuyibo, ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Yace zai nemi tikitin takara a zaɓen gwamnan jihar Ekiti na ranar 18 ga watan Yuni, 2022 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Accord Party (AC).

Mista Famuyibo, ya bayyana matakin da ya É—auka ne yayin zantawa da manema labarai a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, ranar Laraba.

Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin APC, ya soki tsohuwar jam'iyyarsa bisa ƙin baiwa ƴan takarar filin fafatawa har a fitar da ɗan takara ɗaya tilo.

Meyasa ya fice daga APC mai mulki?

Famuyibo yace ya ɗauki matakin ficewa daga APC ne saboda ya cimma burinsa a jam'iyyar AC, da kuma buƙatar mutane da masu ruwa da tsaki na ciki da wajen Ekiti kan ya tsaya takara.

Yace mutanen da suka amince masa da kuma É—umbin magoya baya sun bukaci ya nemi tikitin takara a wata jam'iyya.

Fitaccen ɗan siyasan, haifaffen Ado-Ekiti, yace ya gano shirye-shiryen zaɓen fidda gwani a APC na tafiya ne kan tsarin wanda gwamna ke son ya gaje shi.

Dan haka ba bukatar cigaba da tafiya a haka, ya kuma bayyana cewa, "Ba zai yuwu mu cigaba da tafiya a haka ba, duba da manufofin mu ga jihar mu."

Bello yace APC ce jam'iyyar da ya samu nasarar zama gwamna ƙarƙashinta, dan haka wajibi sai ta kammala babban taronta na ƙasa kafin ya bayyana shirinsa na takarar kujera lamba ɗaya.

Punch ta rahoto gwamna Bello yace:

Mun maida hankali kan babban taron jam'iyyar mu ta APC, kuma da izinin Allah zan ayyana shiga tseren, amma wajibi ne mu nemi takara karkashin wata jam'iyya, kuma ita ce APC."

"Jam'iyyar mu na tafiya kan siraɗi mai kyau ƙarƙashin jagorancin gwamna Mala Buni na Yobe, kwamitinsa sun yi namijin kokari, mu zamu ƙarisa aikin a babban taro."

Yaushe gwamnan zai shiga tseren takara a 2023?

Game da kiran da yan Najeriya, matasa da mata ke masa na ya fito takara, Bello ya ce kowa ya kwantar da hankalinsa, zai amsa kiran su nan ba da jimawa ba.

"Kiran da yan Najeriya, matasa da mata da mutanen Najeriya dake kowane sashi na duniya cewa na fito takara domin É—ora wa daga inda shugaba Buhari zai tsaya, tabbas zan amsa kiransu da zaran mun kammala taro."

Ya kuma yaba wa kwamitin rikon kwarya ƙarkashin Mala Buni, saboda namijin kokarin da suka yi kan babban taron, tare da tabbatar da cewa APC zata ƙara zama da gindinta bayan taron.

Yan ta'addan sun yi wa jiga-jigan jam'iyyar É“arna, inda suka kashe mutum biyu, kuma suka jikkata wasu da dama, suka yi awon gaba da mutum É—aya.

Wata majiya daga cikin mahalarta taron, ya bayyana cewa an kira taron ne domin sasanci tsakanin bangarorin jam'iyyar APC a kokarin da ake na haÉ—a kai baki É—aya.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN