A baya-bayan nan an ga wasu mutane biyu mafi tsayi a duniya a wani gari mai suna Ash Sharqia da ke birnin Alkahira na kasar Masar.
Shahararren mai yawon bude ido Joe Hattab ne ya gano ’yan uwan biyu kuma sun ja hankalin masu amfani da intanet da tsawonsu mai ban tsoro.
Kullum kara girma suke
Namijin mai suna Muhamed Shahat ya bayyana cewa an haife shi ne daidai da kowa amma ya fahimci yana saurin girma tun yana dan shekara 14.
Yanzu yana da shekaru 34, matashin ya kai tsawon mita 2.47, kusan rabin mita kenan kasa da mutumin da ya fi kowa tsayi a duniya wato Sultan Kösen wanda ke da tsawon mita 2.51.
Saboda girmansa da tsawonsa, Muhamed ya koka da yadda masu daukar ma’aikata suka ki daukarsa aiki, wanda hakan ya sanya shi rashin samun aikin yi.
Wani abin sha'awa shi ne, saurayin ya bayyana cewa har yanzu kara girma yake, haka nan 'yar uwarsa Huda da ke tsayin mita 2.40.
Mahifiyarsu na neman taimako
Da take tabbatar da furucin Muhamed, mahaifiyarsa ta bayyana wa Joe Hattab cewa ta haifi 'ya'yan nata kamar kowane yaro amma abin mamaki sun fara girma mara misaltuwa tun daga shekaru 12 da 14.
Ta koka kan yadda tsayin su ya hana su wasu abubuwa da dama kuma ta bukaci mutane su kawo agaji ga 'ya'yanta.
A cewarta, suna bukatar samun waraka don dakatar ci gaba da girman da suke yi cikin sauri.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari