Mazambaci: Kotu za ta yanke wa Hushpuppi hukunci a ranar Valentine a Amurka


Ofishin Babban Antoni na yankin California ta ce za a yanke wa Ramon Abbas, mazambanci na kasa da kasa da aka fi sani da Hushpuppi, hukunci a ranar masoya ta duniya wato Valentine, The Punch ta ruwaito.

A cewar BBC Pidgin, Thom Mrozek, direktan watsa labarai na kotun, ya kuma bayyana cewa ana daf da karkare shari'ar ta Hushpuppi.

Kotun ta tsayar da ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 domin yanke wa Mr Abbas hukunci," in ji shi.

Amma, mai magana da yawun kotun bai bada wani karin bayani ba dangane da tsawon shari'ar da hukuncin da za a zartar.

Hushpuppi, wanda ya yi suna saboda rayuwa irin da ta manyan yara, ya shiga hannun hukuma na a UAE a watan Yunin 2020 tare da wasu abokan aikata laifinsa su 11 kan zargin kutsen intanet, damfara da zamban banki.

An mayar da shi Amurka don yi masa shari'a ne bayan yan sandan na UAE sun fitar da wani faifan bidiyo mai lakabin 'Fox Hunt 2' inda ake zarginsa da damfarar mutane miliyan 1.9 kudin da ya kai Naira biliyan 168.

Daga bisani 'babban yaron' ya amsa laifin karkatar da kudade, hakan na nufin ana iya yanke masa hukuncin da ya kai daurin shekaru 20 a gidan gyaran hali.

Hushpuppi ya yi ikirarin ya bawa Abba Kyari cin hanci

A watan Yulin 2021, sunan Hushpuppi ya sake karade kafafen watsa labarai a lokacin da ya yi ikirarin cewa ya bawa Abba Kyari, mataimakin kwamishinan yan sanda, cin hanci don ya kama, Chibuzo, mazabanci da suke gasa.

Duk da cewa Abba Kyari ya musanta zargin, yan sandan FBI suka yi ikirarin cewa dan sandan ya hada baki da Hushpuppi domin kama Chibuzo.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN