Wani faifen bidiyo da ke yawatawa a intanet ya nuna yadda wasu da ake zargi yan Yahoo ne suka yi bayan gari kuma suka ci bayan garin da suka yi.
Faifen bidiyon da shafin Jaridar isyaku.com ya gani ya nuna yadda wasu matasa suka zazzalo wandonsu suka duka suka yi bayangari kuma suka ci kashin da suka yi a bainar jama'a, a magamar IMSU da ke birnin Owerri na jihar Imo ranar 26 ga watan Janairu.
Wannan lamarin ya faru ne da rana kiri-kiri a bainar jama'a.
Daya daga cikin samarin ya zo da burodi, ya diba burodin ya hada da kashi da ya yi ya ci kuma ya mika wa abokins wanda shi ma ya ci.
Yayin da wannan lamarin ke faruwa, daya daga cikin samarin yana daukar bidiyon abokansa da wayar salula.
A kudancin Najeriya musamman a yankin inyamurai, harkai yan Yahoo ya zarce tunanin ynn Najeriya. Kasancewa sukan yi abin da hankali ba zai dauka ba domin ganin sun cika ka'idodin matakan tsarin tsaface-tsafacensu domin neman biyan bukata na samun kudi dare daya.
Kalli bidiyo a kasa:
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook facebook.com/isyakalabari