Maciyi amana: Allah ya tona asirin dansanda da ke sayar wa yan kungiyar asiri makamai a jihar Kwara, duba abin da ya faru


Yansanda daga sashen Inspector-General of Police Intelligence Response Team ( IRT) sun kama wani dansanda mai shekara 38 a Duniya mai suna Haruna Yusuf bisa zargin sayar wa yan kungiyar asiri makamai a jihar Kwara. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Shida daga cikin yan kungiyar asiri ta Aiye Confraternity na daga cikin wadanda suka kaddamar da miyagun hare-haren rashin Imani kan jama'a a yankin Omu Aran da kewaye.

Sergeant Haruna Yusuf dansandan sashen kula da ababen hawa (Traffic Section) ne a ofishin yansanda na Omu Aran ya sace makaman ne daga tsohon jami'in dansanda da yan sanda ke kira "station officer" a cewa hafsan yansanda DPO na ofishin.

Yansandan sashen IRT na jihar Osun suna bincike ne kan wani dan kungiyar asiri bisa aniyar kungiyarsa ta kaddamar da miyagun farmaki a cikin jihar. Lamari da ya kai ga bankado asirin yadda Sajen Haruna ke taimaka masu da makamai.

Kuma sakamakon haka bincike ya kai ga kame kame da dama ciki har da sauran yan kungiyoyin asiri.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN