Rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Neja sun kama wani matashi mai suna Abubakar Mohammed Buba da laifin kashe mahaifinsa.
Jaridar Punch tace ‘yan sanda na zargin wannan matashi Abubakar Mohammed Buba mai shekara 25 da hannu wajen hallaka tsohon da ya haife shi.
Ana tuhumar Abubakar Mohammed Buba da biyan wani abokinsa kudi N110, 000 domin ya kashe mahaifinsa, wannan ya faru ne a Chachanga, a jihar Neja.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun yace Bida ya amsa laifinsa, yace ya yi haka ne saboda ya ci gadon dukiya.
A jawabin da DSP Wasiu Abiodun ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana yadda aka tsinci gawar marigayin da wanda aka biya kudi domin ya aika shi barzahu.
Ya yi ikirarin ya yi wannan laifi ne saboda ya yi maza ya gaji dukiyar mahaifinsa.” - Wasiu Abiodun
Mai magana da yawun bakin jami’an tsaron yace an kashe Mohammed Buba mai shekara 52 a Duniya, aka kuma jefar da gawarsa a cikin leda a wata bola.
Rahoton da Tribune ta fitar a ranar 6 ga watan Junairu, 2022 yace matashin ya kai ‘yan sanda har zuwa inda aka jefar da gawar mahaifin na sa a Tagwai-Dam.
Wannan matashi da ya shiga hannun hukuma yace ya dauki hayar wani Aliyu Muhammed ‘dan shekara 26, ya taimaka masa wajen kashe mahaifin na shi.
Buba ya kuma biya Mista Aliyu Muhammed kudi N100, 000 domin ya yi wannan danyen aiki. Yanzu haka ana neman Muhammed, amma an rasa inda yake.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka