Labarin yadda uban gida ya kashe yaronsa da duka bisa zargin sace masa N1000 a shago, duba yadda lamarin ya faru


Yansanda masu bincike na sashen State Criminal Investigation Department (SCID), Panti, Yaba, da ke birnin Lagos suna neman wani mutum mai suna Alloy ruwa a jallo bisa zargin kashe yaro mai yi masa aiki a shago.

Lamarin ya faru a No 2 Salako street daga Oyo Agoro street a Ogba, da ke birnin Lagos ranar 10 ga watan Jamairu

Ana zargin Allaoy wanda ke sana'ar sayar da gas na dafa abinci ya yi wa yaronsa mai koyon sana'a mai suna Sunday duka har ya mutu bisa zarginsa da sace masa N1000.

Rahotanni na nuni da cewa Alloy ya tayar da Sunday dan shekara 12 a Duniya da tsakiyar dare lokacin da yake barci, kuma ya tuhume shi da sace masa N1000. Bayan Sunday ya musanta zancen ne Alloy ya azabtar da shi kuma ya dinga yi masa duka har rai ya yi halinsa.

Makwabta sun yi kokarin ceton Sunday amma uban gidansa Alloy ya riga ya rufe gate da kofar shiga.

An gano gawar Sunday da misalin karfe 9 na safe. An nemi Alloy an rasa bayan ya je shagons tun karfe 7 na safe ya kwashe kudinsa kuma ba a sake ganinsa ba.


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN