Gwamnatin tarayya ta dage dakatar da ayyukan kafar sadarwar Twitter a Najeriya bayan amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, The Cable ta rahoto.
Shugaban Kwamitin Fasaha na Najeriya kan hulda da Twitter da Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi, CCIE ne ya sanar da matakin dage dokar.
Kashifu, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce an amince da hakan ne biyo bayan wata takarda da ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim ya rubuta wa shugaban kasa Buhari
Gwamnatin tarayyar Najeriya (FGN) ta umurce ni da in sanar da jama’a cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR, ya amince da janye dakatarwar da aka yi wa kamfanin Twitter a Najeriya daga karfe 12 na daren yau, 13 ga watan Janairu, 2022.
“An amince da hakan ne biyo bayan wata takarda da mai girma ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim ya rubutawa shugaban kasa.
"A cikin takardar, Ministan ya sabunta ya kuma nemi amincewar shugaban kasa don dage dokar bisa shawarar kwamitin fasaha na Najeriya kan Twitter."
Mohammed ya sanar da hakan ne bayan taron majalisar zartarwa ta kasa da suka yi ta yanar gizo wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.
A yayin bada bayanin sasancin gwamnati da Twitter, kamar yadda The Nation ta ruwaito, minsitan yace tuni Twitter ta amince da kusan dukkan sharuddan da Najeriya ta saka mata.
Legit Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka