Kannywood ta yi jihadi: Wani mutum ya Musulunta bayan ya kalli fim na Izzar so (Bidiyo)Jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa, kuma furodusam shirin 'Izzar So' mai dogon zango, Lawan Ahmad, ya ce wani bawan Allah ya karbi shahada sanadin kallon shirin.

Jarumin ya faɗi wannan kyakkyawan labari ne a wani sakon bidiyo da hotonsa da mutumin, wanda ya sanya a shafinsa na Instagram.

A cikin bidiyon, mutumin ya karɓi kalmar shahada wacce ke shigar da wanda ba musulmi ba zuwa cikin ni'imar musulunci, a kusa da jarumi Lawan Ahmad.

Jarumin yace:

"Masha Allah, a yau ne muka yi babban kamu a musulunci, inda wannan bawan Allah ya shiga musulunci saboda kallon Izzar So da yake yi."

Shin mutumin dan ina ne?

Lawan ya ƙara da cewa wanda ya karbi musuluncin ya fito ne daga ƙaramar hukumar Idom Ikon, dake jihar Cross River, kuma ya amince da sunan jarumin shirin, 'Umar' a matsayin sunansa na musulunci.

"Tun daga ƙaramar hukuma Idom Ikon ta jihar Cross River ya taho, yanzu haka ya karbi addinin musulunci. Kuma yanzu haka sunasa ya koma Umar daga John."

Daga karshe Ahmad Lawan, ya yi addu'ar cewa Allah ya sa ya karbi addinin Musulunci a sa'a, kuma Allah ya sa Addinin ya amfane shi da al'umma baki ɗaya.

Lawan Ahmad da sabon musulunta

Masha Allah: Wani mutumi ya musulunta sanadiyyar kallon shirin Kannywood mai dogon Zango Hoto: @lawanAhmad Source: Instagram

Shirin Izzar So, wanda har yanzun ake cigaba da yinsa, ya ƙunshi manyan jarumai da suka haɗa da, Ali Nuhu (Matawalle), Lawan Ahmad (Umar Hashim), Aisha Izzar So (Hajiya Nafisa) da sauran su.

Jarumar Kannywood, Sadiya Kabala, ta koka kan yadda mutane ke da taurin bashi idan ka amince ka ba su kayan ka.

Jarumar tace da kasuwanci ne suke samu suna tsira da mutuncin su, musamman idan suka daina harkar shirin fim.

 Daga Jaridar yanar gizo na shafin

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN