Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya nada sanannen jarumin masana'antar Kannywood, Mustapha Naburaska, matsayin mai bada shawara a kan farfaganda.
Jaridar isyaku.com
Falalu A. Dorayi, jarumi kuma mashiryin fina-finai ne ya wallafa hakan a shafinsa na Instagram a ranar talatin ga wata wacce ta zama ranar Lahadi.
Ya taya jarumin murna tare da yi masa fatan alkhairi.
A cewar Dorayi, an gabatar da bikin nadin a lokacin da aka yi liyafar cin abincin dare wacce a aka gudanar a gidan gwamnatin Kano da maraicen ranar Asabar.
A baya dai, ana ganin Naburaska a matsayin wanda ba ya yin tafiyar Gwamna Ganduje, inda hatta wakoki da bidiyoyi ya sha daukar nauyi na dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, gabanin zaben 2019 da ya gabata a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Amma kuma ko kafin nadin, Naburaska ya ce a yanzu sun samu maslaha da gwamnan kuma ya ce ko a baya wasu miyagu ne suka shiga tsakaninsu domin hana ruwa gudu.
A wallafar Falalu Dorayi, ya ce:
“Muna godiya da wannan mukamai guda biyu. 1. Senior Special Assistant Kannywood (Malam Musa Khalid) 2. Special Adviser on Propaganda to the Governor (Mustapha Badamasi Naburaska).
“Jiya [Asabar] bayan kammala dinner da Governor Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mika mukamai guda biyu ga ’yan uwanmu.
“Daga yau duk wani mai bukata ko matsala tsakanin Kannywood da gwamnati to a nemi wadannan mutum biyu. Allah Ya taya ku riko, Ya baku ikon gamawa cikin amana da alkairi,” inji Falalu Dorayi.
Kano: Sadiya Haruna ta sha da kyar hannun Ƴan daba, sun yi yunƙurin watsa mata acid
A wani labari na daban, fitacciyar jaruma, Sayyada Sadiya Haruna, ta saki wani bidiyo inda ta koka kan wasu 'yan daba a birnin Kano sun yi yunkurin watsa mata acid a fuska a ranar Juma'a, 28 ga watan Janairu.
Cike da tashin hankali yayin da ta ke kuka tare da ihu ta yi bidiyon a cikin mota, inda wani matashi wanda ta kira da Besty ya ke jan ta.
A cewar Sadiya Haruna kamar yadda ta wallafa a shafin ta na Instagram, ta taso daga shagon ta inda ta ce wa kanin ta za ta biya kanti domin siyayya, shi ya karasa gida kafin ta iso.
Source: Legit.ng
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook facebook.com/isyakalabari