Tinubu ne zai ci zaben 2023 cewar hasashen wani Malami, duba ka gani


Shugaban cocin superintendent of Glorious Vision World Outreach Ministries, Rev (Dr.) David Oyediran, ya yi hasashen cewa babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai shugabanci Najeriya.

Jaridar isyaku.com

A cewar faston, Tinubu na daya daga cikin yan tsirarun mutane da za su iya gyara kasar a matsayin shugaban kasa.

A watan nan ne dai tsohon gwamnan na Lagas ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.

Oyediran a jawabinsa mai taken ‘Nufin Allah kan Najeriya’, ya ce Allah ya nuna masa hakan ne bayan yiwa kasar gagarumin addu’a, The Nation ta rahoto.

A cewarsa:

“Allah ya bayyana cewa a cikin yan tsirarun mutanen da za su iya jagoranci da dawo da muradin yan Najeriya shine Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

“Allah ya ce zai jagoranci Najeriya bisa kundin tsarin mulki kuma zai inganta tattalin arzikin kasar.

“Allah ya kuma fada mani wasu sakonni na sirri zuwa ya Asiwaju Tinubu wanda za su jagorance shi da taimaka masa wajen cika nauyin da Allah zai daura masa kan Najeriya idan jam’iyyarsa ta zabe shi a matsayin dan takararta.”

Oyediran ya magantu kan hasashensa na baya wanda duk sun faru

Da yake tuna hasashensa na baya da suka zama gaskiya, Oyediran ya ce:

"Wasu shekaru da suka wuce lokacin da Cif Michael Otedola ya yi takarar gwamnan jihar Lagas a karkashin jam'iyyar NRC, Ubangiji ya nuna mani cewa Cif Otedola zai yi nasara a zaben kuma ya zama gwamnan jihar Lagas.

"Mutane da yawa basu yarda ba saboda manayn yan siyasan da ke bayan Cif Dapo Sarumi da Farfesa Agbalajobi na jam'iyyar SDP wadanda suma suke takara.

"A karshen zaben, maganar Allah ya afku kamar yadda aka sanar mani sannan Cif Michael Otedola ya lashe zaben ya zama gwamnan jihar Lagas."

Ya kuma ce a 1993 Allah ya bayyana masa cewa MKO Abiola zai lashe zabe sannan za a soke shi, kuma hakan ya faru.

Legit 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN