Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa, gagararen dan bindiga Bello Turji da mutanensa sun hanzarta barin dajin da suke saboda jiragen NAF suna ta ragargazar dajin Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi kuma suna tafiya kudancin Zamfara.
Majiyoyin sun ce an hango matasan dauke da makamansu inda suka kafa tantina a dajin Gando da ke karamar hukumar Bukkuyum ta jihar.
Gando yanki ne da ke kusa da daji kuma yana da nisan kilomita 35 zuwa garin Bukkuyum, headkwatar karamar hukumar. Yankin da wasu kauyuka masu yawa duk suna karkashin mulkin 'yan bindiga.
Mazauna yankin sun sanar da cewa sojojin kasa sun kafa bukkokinsu a yankin a cikin dajin. Sun ce 'yan ta'addan suna yawo a kan babura tare da wasu da ke yawo a kasa tare da shanunsu.
Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari