Rahotanni daga karamar hukumar Zuru a kudancin jihar Kebbi na cewa Masarautar Zuru ta dakatar da shugaban Yan sa kai na Masarautar Mr. John Mani daga mukaminsa nan take.
Shafin labarai na Jaridar isyaku.com ya samo cewa Sani Ibrahim Navy ne sabon jagoran Yan sa kai na Masarautar Zuru.
Mun samo cewa hakan ya biyo bayan wani zama da aka yi ne tsakanin manyan jami'an tsaro na Masarautar Zuru kan lamarin.
Sakamakon haka aka dauki matakin dakatar da John Mani daga mukaminsa.
Kazalika mun samo cewa matsalar ta taso ne bayan John Mani ya ziyarci jihar Zamfara kan lamari da ya jibanci tsaro bisa gayyatar mahukunta a jihar Zamfara ba tare da sanar da Masarautar Zuru ba.
Kuma a ziyarar aka shirya tsarin tsaro da ya shafi jihar Zamfara da ke da iyaka da Masarautar Zuru da ta yi wa jihar Zamfara iyaka daga yankin kudancin jihar Kebbi.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook facebook.com/isyakalabari