Labarin saurayi da ke gudu da wayoyin salula na yan mata bayan sun amince masa da sunan aure, duba yadda yake damfararsu


Rundunar yansandan jihar Kano ta kama wani saurayi da ke yaudarar yan mata da sunan zai aure su amma sai ya gudu da wayoyinsu na salula. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Saifullahi Muhammad, dan shekara 24 mazauni unguwar GRA a birnin Kano, ya sha yaudarar yan mata cewa zai aure su. Kuma yakan isa har wajen iyayen yan mata da sunan aure.

Sai dai bayan an amince masa domin ya dinga zance da yarinya, sai Saifullahi ya karbi waya da ababen amfani daga hannun yan mata lokacin da ake zaman zancen budurwa da mai neman aure.

Amma daga bisani idan ya je gidan yan matan domin zance, yakan ce yarinya ko ta shiga gida ta samo masa ruwa ko wani abin amfani, kafin yarinya ta fito daga cikin gida sai Saifullahi ya gudu da wayarta.

Ya yi wa yan mata fiye da shida irin wannan yaudara kamar yadda ya amsa da bakinsa lokacin bincike na yansanda a Bompai. 

Sai dai bayanai sun ce ya yaudari yan mata da yawan gaske a birnin Kano.

Daga cikin ababen da ya yaudari yan mata ya karba bayan wayoyinsu masu tsada, har da zoben azurfa da na zinari.

Yansanda na ci gaba da bincike.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN