Type Here to Get Search Results !

Bidiyon motar alfarma da gida da wata miloniya ta mutu ta bari babu magada, har sunyi tsatsa


Wani matashi, Steve Ronin, ya wallafa bidiyon wani katafaren gida da aka gina shekarun 1950s. An banzatar da gidan bayan rasuwar mai gidan a shekara ta 2000. 

Da yake zagayawa a gidan, Steve ya bayyana cewa gidan ba shi da fasali ko tsari wahalan yi. Daya daga cikin 'yan tawagarsa ya daki bangon gidan kuma sunji motsi. 

Hoton cikin falon ya nuna wasu tsofaffin kujeru da kayan daki. Mutumin ya ce kamar an samu baƙi sun kai ziyara kwanan nan, watakila masu ɗaukar hoto. 

Daga baya an gano cewa motsin da aka ji ashe dabba ne. An gano wani karamin gado a cikin gidan da wasika da aka rubuta ana tambayar mai gidan ko yaya jikinta. 

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, sama da mutum miliyan uku ne suka kalli bidiyon tare da dubban masu dangwala like. 

Latsa nan la kalli bidiyo:

https://mobile.facebook.com/steveroninofficial/videos/367417684885193/

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies