Mista Buhari ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels da aka watsa a ranar Laraba 5 ga watan Janairu, Premium Times ta rahoto.
Ya ce ya tattauna da ministan noma domin dawo da hanyoyin burtali da aka yi a jamhuriya ta farko musamman a Arewacin Najeriya.
Yan Najeriya da dama sun soki wannan manufar, inda suka ce maimakon haka a sanya makiyaya su yi kiwon shanunsu a wuraren kiwo kebabbu.
Daruruwan mutane ne ake kashewa duk shekara a fadin Najeriya a tashin hankalin da ke tsakanin makiyaya da manoma.
A tattaunawarsa, shugaba Buhari ya yi batutuwa da dama da suka shafi kasar nan, musamman ta fuskar yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka