Rahotanni daga birnin Gwandu a karamar hukumar Gwandu na jihar Kebbi na cewa fusatattun matasa sun yi wa wani mutum da ake zargi da satar babur dukan ajali har ya bakonci barzahu kuma aka banka wa gawarsa wuta.
Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa wani mazauni garin Gwandu da baya son a ambaci sunansa ya ce wanda lamarin ya rutsa da shi sananne ne wajen addabar jama'ar gari da kewaye da sace-sace.
Lamarin ya faru ne ranar Talata 4 ga watan Janairu da dare.
Kazalika majiyar ta yi zargin cewa wanda aka kashe bai dade da fitowa daga gidan gyara hali ba, kuma sai ya aikata wannan danyen aiki.
Lamari da majiyar ta ce ba zai rasa nassaba da kara fusata matasa ba wajen daukan doka a hannunsu.
Sai dai wani faifen bidiyo da ke yawatawa a intanet ya nuna yadda gawar barawon ke ci da wuta.
Kalli bidiyo a kasa:
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka