An fara shirin kara kudin man fetur gadan-gadan, duba ka gani


Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya da gaske take yi a kan batun janye tallafin fetur.

Jaridar Punch ta rahoto Zainab Ahmed ta na cewa Mai girma Farfesa Yemi Osinbajo zai jagoranci zaman da za ayi da kungiyar ‘yan kwadago a kan lamarin. 

Mataimakin shugaban kasar zai jagoranci tattaunawar da gwamnati za tayi da NLC da masu ruwa da tsaki da nufin rage radadin da jama’a za su shiga. 

Gwamnatin tarayya ta na tunanin rabawa marasa karfi N5, 000 da kuma shigo da wasu dabarun da za su sa cire tallafin man fetur din ba zai yi tasiri sosai ba. 

Kwamitin Yemi Osinbajo aka ba alhakin shawo kan ‘yan kungiyar kwadago wanda ba su goyon bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ta kara farashin mai 

Ahmed tace kwamitin zai duba abin da ya fi dacewa ayi wa marasa hali bayan an dawo hutun sabuwar shekara, inda za a ji ta bakin NLC da sauran jama’a. 

Da take amsa tambayoyin ‘yan jarida, an rahoto Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin ta na cewa gwamnati za ta cire hannunta a kan fetur. 

Zainab Ahmed tace kasafin kudin shekarar bana ya yi aiki da dokar Petroleum Industry Act 2021. 

Game da batun rabawa talakawa N5, 000 domin su samu kudin zirga-zirga, Ahmed tace har yanzu ana duba yiwuwar yin hakan ne, ba a tabbatar da tsarin ba. 

Baya ga maganar raba kudin, Ministar tattalin arzikin tace akwai wasu dabaru da gwamnati ta ke dubawa domin ganin tashin mai bai taba maras karfi sosai ba. 

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN