Ba zan bari wani ya hada 'yan daba su dauki makami ba, inji Buhari


A ranar Alhamis, 20 ga watan Janairu, shugaban kasa Muhammadu Buhari, a garin Kafanchan, jihar Kaduna, ya yi gargadin cewa ba za a bari wani ya tara rundunar ‘yan daba domin tilastasu kan wasu jama’a ba.

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabinsa a fadar Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammadu Isa 11, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Sai dai Buhari ya jaddada kudirinsa na dunkule tsarin siyasar kasar domin inganta rayuwar al’umma saboda al’ummar kasar.

Jaridar Sun ta ruwaito Buhari na cewa:

"Muna yin kokarinmu don karfafa tsarin don amfanin jama'a saboda suna da mahimmanci."

Don haka, ya yi magana game da amfani da 'yan sanda da sojoji, wajen magance matsalolin tsaro, inda ya bukaci 'yan Najeriya da su bunkasa amincewa da hukumomin tsaro don gina tsarin "ba tare da hargitsi ba."

Babu wanda ya kamata a bar shi ya tara rundunar ‘yan daba don tilasta kansa kan mutane."

Shugaban ya yabawa gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna bisa nasarorin da ya samu wajen samar da ababen more rayuwa, bayan kaddamar da sabuwar hanyar Dan Haya, titin Katsina, da titin fadar sarki a Kafanchan.

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara Kaduna a ranar Alhamis, inda ya tuna da yadda ya tsallake rijiya da baya da aka dasa masa bam a kusa da gadar Kawo, a lokacin da yake tafiya jihar Katsina a watan Yulin 2014.

Jaridar Vanguard ya ruwaito Buhari wanda yake a sabuwar gadar Kawo da gwamnatin El-Rufai ta gina, ya ce:

“An yi yunkurin tayar da bam a nan… akwai wata kasuwa a kusa."

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN