Babban abin da zai kawo mana cikas a babban zaben 2023 dake tafe, shugaban INEC


Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana damuwarsa kan ƙaruwar matsalar tsaro yayin da zaben 2023 ke ƙaratowa.

Yakubu ya yi wannan furuci ne a wurin taron kwamitin tsaro na haÉ—in guiwa (ICCES), wanda ya gudana a hedkwatar hukumar INEC dake Abuja, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.

Shugaban INEC ya kuma yaba wa hukumomin tsaro bisa namijin kokarin da suka yi wajen tabbatar da tsaro yayin zaben gwamnan jihar Anambra.

Sai dai yace yawaitar matsalar tsaro a sassan Najeriya, wata barazana ce kuma abin damuwa game da zaɓen 2023.

Kazalika, Farfesa Yakubu, ya bayyana zaɓen da hukumarsa ke fuskanta a cikin shekarar nan 2022 na wasu jihohin Najeriya.

Shugaban INEC yace:

"Game da zaben ƙarewar wa'adi, muna da manyan zaɓukan dake tafe cikin wannan shekarar 2022. Zaɓen gwamnan jihar Ekiti zai gudana ranar 18 ga watan Yuni, 2022 da kuma na jihar Osun ranar 16 ga Yuli, 2022."

"Sannan akwai zaben kananan hukumomi na Abuja da za'a gudanar nan gaba kaɗan. A mako mai zuwa kwamishinan zaɓe da na yan sanda za su mana bayani kan yanayin tsaro a faɗin Abuja."

Daga cikin waÉ—an da suka halarci taron, akwai mai bada shawara kan tsaro, Babagana Monguno, darakatan hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi, da sufeta janar na yan sanda, Usman Baba.

Bola Tinubu, ya faɗi ɗaya daga cikin muhimman kudirinsa da zai fara aiwatar wa yan Najeriya da zaran ya zama shugaban ƙasa a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Legas yace gwamnatinsa zata biya wa yara yan Sakandire kuÉ—in zana jarabawar WAEC.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN