Abun mamaki: Rahotun yadda makamai da harsashi 178,459 na yan sanda suka bace a Najeriya cikin shekara daya - Inji AuGF
The Nation tace wani rahoto da babban mai binciken gwamnatin tarayya ya fitar, yace makamai iri-iri kusan 178, 459 sun bace daga rumbun ‘yan sanda 

Binciken da ofishin AuGF ya gudanar na shekarar 2019 ya nuna cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ba su sanar da hukuma game da bacewar makaman ba. 

Haka zalika binciken ya zargi shugabannin ‘yan sanda da kin bada bayani kan makamai da harsasun da suka tashi aiki ko wadanda ba za su iya aiki da kyau. 

Jaridar Vanguard tace hakan zai iya jawo a rika amfani da makamai ta hanyar da ba ta dace ba. 

Wannan bayani da AuGF ya yi, ya na dauke ne a rahoton binciken da aka yi a kan duka ma’aikatu da kuma hukumomin gwamnatin tarayya a shafi na 383 zuwa 391. 

Babban mai binciken gwamnatin tarayya, Adolphus Aghughu ya sa hannu a binciken a watan Satumban 2021, kuma an aika rahoton zuwa ga akawun majalisar. 

Wannan danyen aiki da rundunar ‘yan sandan Najeriya tayi, ya sabawa sakin layi na 2603 na dokokin tarayya. Hakan ya na iya zama barazana ga harkar tsaro. 

Zuwa Disamban 2018, bindigogi da makaman ‘yan sanda da aka rahoto cewa sun bace sun kai 178,459. Daga cikin wannan adadi akwai bindigogin AK-47 88,078. 

Sannan akwai kananan bindigogi 3,907 da aka rasa inda suka shiga zuwa Junairun 2020. Bayan haka akwai zargin badakalar kwangiloli da aka tafka a gidan NPF. 

Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN