Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasan Najeriya suyi amfani da ilmin da suka samu a makaranta da wayewa wajen inganta kawunansu sabanin dogaro kan aikin gwamnati.
Buhari ya bayyana hakan ne yayin hira ta musamman da gidan talabijin ChannlesTV ranar Laraba.
"Na so idan suka je makaranta; suka yi kokari; suka samu digiri, kada suyi tunanin dole ne sai gwamnati ta basu aiki," ya bayyana.
"Ka nemi ilimi ne saboda mai ilimi ya fi mara shi, ko wajen fahimtar matsalolin kai. Saboda haka ba a neman ilimi don gwamnati ta bada aiki ko kuma abinda turawan mulkin mallaka suka dasa mana a kai na cewa sai ka yi mota, ka yi gini, kana zuwa aiki karfe 8 ka dawo karfe 2."
Bayan haka, Buhari ya yi magana kan wasu lamura wanda ya hada da rashin rattafa hannu kan dokar zabe.
Buhari ya ki rattafa hannu kan dokar saboda tsarin yar tinke da aka sanya cikin dokar.
A hirar, ya ce zai rattafa hannu muddin majalisar dokokin tarayya tayi gyaran da ya kamata.
"Abinda na fadi shine a baiwa mutane zabi. Bai kamata mu ce wajibi ne ayi yar tinke ba; ya kamata akwai ittifaki da na deleget."
Yayinda aka tambayesa ko zai rattafa hannu idan yan majalsan suka yi canjin, ya tabbatar da cewa, "A zan yi, zan rattafa hannu."
"Ya kamata akwai zabi, ba zai yiwu ku yiwa mutane kama karya ba kuma kuce kuna demokradiyya. Ku basu wasu zabin saboda su zaba."
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yiwa yan Najeriya iyakan kokarinsa kuma yana sa ran idan ya sauka daga mulki zasu fadi hakan da kansu.
Shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayin hirarsa a gidan talabijin na NTA da aka haska ranar Alhamis.
Buhari yace:
"Abinda nike sa ran yan Najeriya suce shine mutumin nan ya yi iyakan kokarinsa."
Source: Legit.ng
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka