Wani mahaifi mai shekara 56 ya sha duka har ya mutu a hannun 'ya'yansa maza guda uku bayan sun yi zargin cewa ya sace masu wayar salula da suka hada kudi suka saya.
Lamarin ya faru ne a kauyen Shikangania da ke mazabar Lurambi , a gundumar Kakamega da ke kasar Kenya,
Yaran dai yan makarantar sakadari ne su biyu tare da wani kaninsu da ke ajin framare.
Rahotanni sun ce yaran sun gayyaci mahaifinsu ne zuwa wajen makoki da aka shirya bayan mutuwar makwabcinsu.
Sai dai yaran sun lallabi mahaifinsu zuwa wajen gari suka halaka shi a cikin daji.
Yan sanda sun kama yaran kuma ana gudanar da bincike.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI