Wata dalibar aji daya a Jami’ar Jihar Taraba (TSU) ta mutu sakamakon gobarar da ta tashi a dakin kwanan daliban.
A cewar gidan talabijin na Channels, dalibar mai suna Enuseh Lawi ta makale ne yayin gobarar a daren Juma’a.
An tattaro cewa gobarar ta taba wasu sassa na Zenith Hostel da Enuseh ta ke zaune har ta mutu.
An ce gobarar ta tashi ne yayin da dalibar ke kwance tana bacci, TheCable ta ruwaito. An ruwaito daga majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin na cewa wasu dalibai mata suka balla dakin kafin a samu damar shiga.
An ce an garzaya da ita asibitin kwararru na Jalingo inda aka ce ta rasu. Gobarar da ta shafi wasu sassa na dakin kwanan dalibai, ta jawo asarar dukiya da sauran kayayyaki masu daraja.
A cewar majiyar: “An gaya mini cewa matar ta tafi karatu dare saboda jarrabawarta kuma ta dawo a gajiye, don haka ta yi barci.
“Musabbabin wannan gobarar ta samo asali ne daga wani soket na wutan lantarki wanda ya kone kuma ba zato ba tsammani ya kama katifar da ke kusa da ita inda ta bazu ko’ina."
Legit Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI