Type Here to Get Search Results !

Yanzu yanzu: Zanga-zanga ya barke, mutanen gari mata da maza sun ce sai dai soji su kashe su domin sun gaji da wannan mulki, duba dalili (Bidiyo + Hotuna)


Rahotanni daga dajin wani gari a arewacin Najeriya Kanen haki na nuna cewa jama'a maza da mata, yara da manya sun fito zanga-zanga suka tare babbar hanyar mota kan hanyar zuwa Kano kafin garin Yar kara. Lamari da ya haifar da cinkoson daruruwan motoci. Shafin isyaku.com ya samo.

Masu zanga-zangan wadanda wasu ke ta kuka, Mata da maza, suna zargin cewa yan bindiga sun kashe mutane bakwai a garin kuma suka yi wa bayin Allah wulakancin fitar hankali.

Sun kalubalanci sojin cewa su kashe su ko dama can yan bindiga sun riga sun kashe su, sakamakon haka sai dai soji su halaka su gaba daya.

Rahotun bidiyon ya nuna cewa soji na ta kokarin kwantar wa masu zanga-zangan hankali tare da lallashin su.

Kazalika rahotun ya ce wani Bafulatani da ya biyo ta garin ya sha da kyar a hannun fusatattun masu zanga-zangan da suka yi kokarin kashe shi amma soji suka hana.

Latsa nan ka kalli bidiyo:

https://www.facebook.com/1086336452/posts/10220841405040038/?app=fbl

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies