An kuma: Yan bindiga sun sake aikata mugun aiki, sun kone mutum da ransa, duba yadda ta faru


Mako biyu bayan abin da ya faru na ƙona fasinjoji a cikin mota a jihar Sokoto, wasu miyagun yan bindiga sun sake kona mutum a ƙaramar hukumar Faskari, jihar Katsina

A cewar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, wanda shine mamba mai wakilaltar Faskari, sun kona mutumin da ransa a cikin motarsa. 

Ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa wannan lamarin É—aya ne daga cikin hudu da suka faru cikin mako É—aya a yankin. 

ÆŠan majalisar ya kara da cewa an kashe wasu mutane da dama sannan kuma aka yi awon gaba da wasu. 

Premium Times ta rahoto a jawabinsa yace:

 "Sun kai hari kauyen Kwakware inda suka sace mutum 17 mafi yawancin su mata ne. Washe gari suka tare direba, suka kashe shi, ta hanyar kona shi da ransa a cikin motarsa."

 "A jiya Talata kaÉ—ai, sun kashe mutum bakwai kuma suka yi awon gaba da wasu biyar. Kuma wurin da aka kai harin ba shi da nisa da madakatar binciken ababen hawa na sojoji." 

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN