Yan sandan ofishin Zuba da ke babban birnin tarayya ranar Juma'a sun harbe wani jami'in hukumar tsaro na farin kaya DSS, yayin wani samame da suka kai kan al'umman Dakwa. Jaridar Daily trust ta wallafa.
Rahotun Jaridar ya ce jami'in DSS da ba a gane ko waye ba kawo yanzu matafiyi ne ko da lamarin ya rutsa da shi.
Akalla mutum 37 ne aka kama lokacin wannan samame da Yan sandan suka gudanar da misalin karfe 8:00pm na dare.
Wani mazauni unguwar da lamarin ya rutsa da shi kasancewa cikin wadanda yansandan suka kama mai suna Aliyu Ibrahim, ya shaida wa Daily trust cewa wadanda aka kama sun hada da masu suya, Yan acaba, Yan kasuwa da masu shayi.
Ya yi zargin cewa an tsare su suka kwana a ofishin yansandan har wayewar gari, daga bisani aka sake su bayan sun bayar da N5000 kowannensu.
Babban jami'in Dan sanda na ofishin Zuba (DPO), CSP Osor Moses, ya tabbatar da harbe jami'in DSS, ya ce an Kai shi Asibitin koyarwa na Abuja da ke Gwagwalada inda yake samun kulawan Likitoci.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka