An tabbatar da mutuwar mutane shida yayin da mutane biyu ke cikin wani mawuyacin hali a garin Kabete, da ke gundumar Nairobi a kasar Kenya. Shafin isyaku.com ya samo.
lamarin ya faru ne ranar Talata 7 ga watan Disamba bayan wani Dan sanda mai suna Constable Benson Imbasi, ya kashe matarsa bayan ya harbe ta da bindiga a wuya, daga bisani ya fito daga cikin gidansa ya fara harbin bayin Allah ba gaira ba dalili nan take ya kashe mutum biyar. Daga bisani ya juya bindiga ya harbe kanshi har Lahira.
Wata Takarda dangane da lamarin da ta fito daga shugaban sashe, kuma Daraktan Criminal Investigations, DCI, ya ce Dan sandan ya yi marisa kawai ya fara harbi da bindiga kirar AK47 ya kashe wasu samari uku nan take, kuma ya kashe wani dan acaba da ake kiransu matukan Boda-boda a kasuwar N a birnin Kabete.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI