Rikicin jam'iyar APC a jihar Kebbi ya kai ga nada wakilai domin sasantawa a Abuja


Kwamitin uwar jam'iyar APC ta kasa kan sasanta rikicin da ya kunno kai tsakanin yayan jam'iyar APC a jihar Kebbi ya kasa ci wa matsaya a zaman farko da ya yi a jihar Kebbi.

Ranar Laraba 1 ga watan Disamba kwamitin sasanta rikicin cikin gida na jam'iyar APC reshen jihar Kebbi karkashin shugabancin tsohon Gwamnan jihar Nassarawa Abdullahi Adamu, ya isa jihar Kebbi kuma ya sami fuskantar bangarori da ke da korafe-korafe a jam'iyar.

Sai dai sashen harkokin Siyasa na shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa, kwamitin bai ci wa matsaya ba dangane da takaddama da ta kunno kai tsakanin yayan jam'iyar a jihar Kebbi.

Sakamakon haka bangarori da ke da korafe-korafe suka aminta da wakilcin wasu jiga-jigai kuma masu ruwa da tsaki a harkokin jam'iyar na jihar Kebbi domin su wakilce su a Abuja inda ake sa ran kwamitin za ta ci gaba da zamanta kan lamarin.

Wadanda aka dora wa wakilcin su ne 

1. Ministan shari'a Abubakar Malami SAN

2. Sanata Adamu Aliero

3. Gwamna Abubakar Atiku Bagudu

4. Sanata Dr Yahaya

Waiwaye

Jam'iyar APC a jihar Kebbi ta tsunduma cikin wasu manyan rigingimu ne bayan matsaloli da suka kunno kai tsakanin yayan jam'iyar kafin taron Congress na jam'iyar da aka gudanar a jihar.

Kafin wannan lokaci, baraka ta kunno kai bayan dakatarwa da jam'iyar APC reshen jihar Kebbi ta yi wa tsohon shugaban jam'iyar reshen jihar Kebbi tare da Sakataren kudi na jam'iyar, kuma mai hulda da jama'a na jam'iyar ya yi murabus na gaggawa.

Shafin isyaku.com ya samo cewa lamarin ya kai ga wasu yayan jam'iyar sun garzaya babban Kotun jihar Kebbi ta 5 bisa wasu bukatu da suke nema ta hanyar sharia.

Kazalika lamarin ya kai ga tsige Kakin Majalisar Dokoki na jihar Kebbi Alhaji Samaila Kamba.

Bayyanar wani faifen bidiyo da ya nuna wani Sanata kuma babban jigo a jam'iyar APC reshen jihar Kebbi Yana bayani irin yadda ake cire mutane daga mukami ko matsayinsu matukar suna da alaka da wasu manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyar a jihar Kebbi.

A faifen bidiyon, babban dan siyasan ya ce irin kurakurai da jam'iyar PDP ta yi har ta fadi zabe a 2015 shi ne yanzu ake yi a jam'iyar.

Yanzu haka dukan bangarori sun kasa kunne domin sauraron hukunci da shawarwari da Kwamitin sasantawar za ta yi dangane da matsalolin da jam'iyar APC reshen jihar Kebbi ke fuskanta.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN