Yadda masu garkuwa da mutane suka bi mata da miji gona suka sace su


Yan bindiga sun sace wani magidanci, London da matarsa, Blessing Omoru a cikin gonarsu da ke wani kauye a karamar hukumar Obokun a cikin jihar

The Nation ta tattaro bayanai akan yadda miji da matar suke cikin gonarsu da ke kauyen Ori-Omipupa kusa da wuraren Agric, ‘yan bindigan sun yi dirar mikiya su ka hau harbe-harbe da misalin 9pm. 

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa The Nation cewa: “Yan bindiga sun shiga wuraren gonar inda su ka dinga harbe-harbe, ana wannan yanayin ne su ka yi garkuwa da mutanen

. “Masu gadin gargajiya da ake kira Kiriji Heritage Defenders sun samu labari akan harin, shugabansu Ademola Ekundayo tare da yaransa sun bi sawun ‘yan bindigan amma abin ya ci tura don sun je da miyagun makamai ne. 

“Daga baya muka sanar da ‘yan sanda wadanda har yanzu ba su samu sun ceto su ba. Yaran Kiriji su na daji tare da ‘yan sanda.” 

Wata majiya daga jami’an tsaro ta sanar da yadda ‘yan bindigan su ka sace miji da matar da niyyar samun kuadaden fansa daga jama’an garin saboda lamarin ya auku ne tsakanin Esa-Oka da Esa-Odo. 

Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, SP Yemisi Opalola ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kamar yadda ta ce, da misalin karfe 10:45pm wani Moses Imomiuku na titin Ayetoro ya kai rahoto ofishin ‘yan sandan Esa Oke cewa da misalin karfe 10pm wani Andrew Omoru ya sanar da shi cewa an sace iyayensa a gonarsu. 

Kakakin ta ce lokacin da jami’an rundunar ‘yan sandan suka isa wurin sun daura aniyar hada kai da ‘yan sa kai na OPC don ceto wadanda aka sace. 

Yayin hakan ne tace sun samu nasarar ceto babur din wadanda aka sata sannan har yanzu su na ci gaba da kokartawa. 

Source: Legit 


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN