Jami'an hukumar kula da filaye na jihar Kano sun sake rufe ofishin babban lauya, Nureini Jimoh, SAN, wanda ya wakilci bangaren Shekarau ya kuma yi nasara kan bangaren Ganduje a rikicin shugabancin jam'iyyar APC, Daily Nigerian ta ruwaito.
Kwana daya bayan samun nasarar a kotu, gwamnatin jihar Kano ta garkame ofishin lauyan da kwado yayin da shi da wasu ma'aikatansa ke ciki suna aiki.
Bayan kungiyar lauyoyi ta Najeriya, NBA, da jama'a a kafafen watsa labarai sun koka kan lamarin, an bude ofishin a ranar.
Amma Daily Nigerian ta bincika ta gano cewa jami'an gwamnatin sun sake dawowa cikin dare sun sake rufe ofishin. Wata majiya ta ce wannan abin kunya ne ga gwamnatin jihar Kano Wata majiya ta bayyana cewa:
“Da safiyar yau, muka samu rahoton yadda gwamnatin jihar Kano ta kara komawa ofishin kauyoyin don garkame ofishin a karo na biyu. Abin ban mamaki shine yadda ofishin ne kadai dokar gwamnatin ta hau kai. Lamarin ya faru ne da da dare. Wannan abin kunya ne ga gwamnatin jihar Kano kuma zalinci ne.”
Hukumar kula da filayen jihar Kano a ranar Alhamis ta yi bayani akan wannan aikin inda ta ce ta aikata hakan ne ga mai hayar wurin ba lauyan ba. Kakakin hukumar, Murtala Umar ya ce:
“Gwamnatin jihar ta garkame wurin wanda Isiyaka Rabi’u & Sons da ke C14/C16 kan titin Murtala Muhammad ne ke hayar wurin.
“Kwamitin ta ba mai wurin gargadi akan wannan wurin tun ranar 14 ga watan Satumban 2021 kuma ta ba shi damar wata daya tana bukatar ya biya kudin hayar wurin tun 2016 zuwa 2021. “A jiya 1/12/2021, mun garkame wurare talatin daga bangarori daban-daban da ke jihar kamar wasu wurare da ke Zoo road, Zaria road da Ibrahim Taiwo road.”
A cewar kakakin sai da su ka ja kunne kafin su garkame wurin Ya kara da cewa duk wuraren da su ka garkame a titin Murtala Muhammad sai da su ka ja kunne amma ba su samu wata amsa mai kyau ba.
Don haka kwamitin ta yanke shawarar rufe duk wani wuri da bai bi dokokin filaye ba. Don haka ya ce a matsayinsu na masu kula da filaye, takardu sun nuna musu cewa C14/C16 Isiyaka Rabi’u & Sons ne ke hayar wurin ba Barrista Nuraini Jimo ba.
Source: Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari