Gwamnatin Kaduna Za Ta Kori Malaman Sakandire 233


Jihar Kaduna ta bayyana shirin korar malamai 233 da suka gabatar da takardar bogi.


Alhaji Tijjani Abdullahi, shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jiha (KADSUBEB) ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Alhamis.


Shugaban ya ce a wani bangare na alhakin da ya rataya a wuyan Hukumar na tabbatar da cewa a zahiri dukkan malaman sun cancanta da karantarwa, hakan yasa hukumar ta kaddamar da aikin fara tantance takardar shaidar Kammala karatu a watan Afrilun 2021.


Ya ce babban makasudin gudanar da atisayen shi ne tabbatar da cewa malaman sun samu takardun shaidar kammala aikin da ya kunshi muhimman abubuwan da ake bukata na aikin.


Ya ce hukumar ta tantance takardun shaidar kammala karatu 451 ta hanyar tuntubar cibiyoyin da suka bayar da takardar shedar inda tara daga cikin cibiyoyi 13 da aka tuntuba suka bayar da rahoto.

Leadership Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN