Ana fargaban cewa mutane da dama sun mutu bayan Yan bindiga sun buda wa jama'a da ke Sallah a cikin wani Masallaci wuta da bindigogi a kauyen Ba’are da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Niger. Shafin isyaku.com ya samo.
Rahotanni na nuni da cewa Yan bindigan sun buda wa masallata wuta ne a cikin Masallacin yayin da suka tsakar Sallar Asuba.
Kwamishinan yansandan jihar Niger Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce akalla mutane 9 ne maharan suka kashe a wannan farmaki.
Wannan yana zuwa ne kasa da wata biyu bayan Yan bindiga sun buda wuta kan wasu Masallata a cikin wani Masallaci a karamar hukumar suka kashe mutum 18.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI