Gwamna Bello Masari na jihar Katsina ya yi fatali da maganar zaman sulhu da yan bindigan, waÉ—an da suka addabi jiharsa da sauran jihohin arewa ta yamma.
Masari ya bayyana matsayarsa ne yayin zantawa da kafar watsa labarai ta DW hausa, ranar Asabar.
Premium times ta rahoto cewa gwamnan ya maida martani ga wasikar dake yawo ta neman zaman sulhu, wanda gawurtaccen É—an bindiga. Bello Turji, ya aike wa gwamnati.
Gwamna Masari, wanda a baya gwamnatinsa ta rungumi tattaunawar sulhu, yace ba sauran tattaunawar sulhu tsakaninsu da yan bindiga.
Duk da babu adireshin sa a wasikar, Masari ya bayyana cewa abin da wasikar Turji ta ƙunsa ba gaskiya bane.
Gwamnan yace:
"Sulhu da wa? Waye shi da yake neman sulhu ko a tsagaita wuta? Shi babban maƙaryaci ne, bai isa ya faɗa mana yadda za'a zauna lafiya ko sulhu ba."
"Ƙaje ka samu iyalan waɗan da yan bindiga suka kashe, ku nemi sulhu da su, kuga yadda zata kaya. Kuma har da saka wasu sharuɗɗa, waye shi da zai kafa mana sharuɗɗa?"
"Shi ke neman sulhu amma har yana da bakin kafa wasu sharudda da za'a cika."
Tawagar Turji na É—aya daga cikin kungiyoyin yan ta'adda da suka addabi yankin arewa maso yamma da wasu sassan arewa ta tsakiya.
Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka