Dan wata Prinsipal ya banka mata wuta da ranta, duba yadda ta faru


Wani saurayi ya banka wa mahaifiyarsa wuta. Wacce aka banka wa wuta ita ce tsohuwar Principal na Government Girls’ Secondary School, Sabon Wuse da Maryam Babangida Girls’ Science College, Minna, Mrs Comfort Jiya. Dan da ta haifa mai suna Steven Jiya ne ya banka mata wuta da kanshi.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa Madam Comfort tana cikin dakin dafa abinci ne a gidanta da ke unguwar Darusalam a birnin Minna, lokacin da danta wanda ake zargin dan kwaya ne ya dawo daga garin Suleja ranar Litinin 20 ga watan Disamba ya watsa mata fetur kafin ya kyasta mata ashana ta kama da wuta.

Daily trust ta ruwaito cewa matar ta mutu da misalin karfe 3pm na ranar Juma'a 24 ga watan Disamba a babban Asibitin Minna inda take jinya. 

Rahotanni sun ce an kama Steven wanda kafin wannan lokaci ya sha yin yunkurin yi wa mahaifiyarsa lahani kafin ya samu sa'ar kona ta, ta hanyar banka mata wuta. Daga bisani yansanda sun gurfanar da shi a gaban Kotu.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN