Rundunar yansandan jihar Ondo ta kama wani Pasto bisa zargin yi wa wata mata mai juna biyu fyade.
Yansanda sun kama Posto ne bayan matar ta shigar da kara a kan shi ta yi zargin cewa ya yi mata fyade garin yi mata addu'a.
Ta yi zargin cewa Pasto ya bukaci ta shiga wani daki a cikin Mujami'arsa bayan ta yi masa bayanin lalurar da take ji dangane da juna biyu da take dauke da shi.
A cewarta, Pasto ya umarce ta cewa ta shiga wani daki a cikin Mujamiarsa, daga nan sai ya ce zai taimake ta. Sai ya ce ta cire kayanta ta kwanta, kuma ta yi.
Ta ce sai Pasto ya sa yatsar hannunsa a cikin wani mai na shu'umi, sai ya saka yatsar a cikin ala'urarta. Ya ce bai kamata ya aikata wanna ba. Amma tunda mijinta baya nan, zai taimake ta. Daga bisani ya yi lalata da ita.
Ta ce bayan ya gama abin da yake yi ne sai hankalinta ya dawo ta gane hakikanin abin da ya aikata mata.
Sakamakon haka ta kai Kara wajen yansanda.
Kakakin rundunar yansandan jihar Mrs Funmilayo Odunlam, ta tabbatar da kama Pasto kuma ta ce ana gudanar da bincike.
Ta ce bata da cikakken bayanin abin da ya faru a daidai lokacin da Jaridar Punch ta tuntube ta.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI