Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na magance yan bindiga domin kare yan Najeriya daga sharrin su.
Buhari ya yi wannan furucin ne lokacin da tawagar gwamnatin tarayya ta kai ziyarar jaje ga gwamna Aminu Tambuwal bisa kisan matafiya 23 a jihar Sokoto.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin gwamnan Sokoto, Muhammad Bello, ya fitar ranar Asabar, kamar yadda daily Nigerian ta rahoto.
Shugaban tawagar gwamnatin tarayya kuma mai bada shawara kan tsaro, Babagana Monguno, shine ya isar da sakon shugaban ƙasa na jaje da ta'aziyya.
Buhari ya yaba wa gwamna Tambuwal bisa datse tafiyar aiki da ya yi domin karɓan tawagar gwamnatin tarayya duk da ba'a sanar masa a kan lokaci ba.
Yace:
"Mun zo Sokoto bisa umarnin shugaba Buhari, dan jajanta maka da sauran al'umman Sokoto da kuma mai martaba sarkin Musulmi, kan abubuwa mara daÉ—i dake ta faruwa a makonnin da suka shuÉ—e."
"Shugaban ƙasa ya damu sosai kan yadda ake samun faruwar haka lokaci bayan lokaci, wanda ke sanadin rasa rayuwar mutanen da basu ji ba basu gani ba."
"Kowane rai na da muhimmanci, abun na damun shugaban ƙasa yadda mutane ke mutuwa ta hanyar rashin tausayi. Shugaba Buhari na mika ta'aziyyarsa kan yan Najeriya da suka mutu."
Wajibi a hukunta masu hannu a kisan matafiya - Buhari
Monguno ya ƙara da cewa, shugaba Buhari ya jaddada kokarin gwamnatinsa na tabbatar da an kame duk mai hannu a kisan kuma sun girbi abinda suka shuka.
"Buhari ya ƙara jajanta lamarin tare da tabbatar da cewa an cafke duk me alaƙa da wannan kisan na rashin Imani da rashin tausayi kuma a hukunta su."
"Shugaban ƙasa ba ya jin daɗin halin da yan ƙasa suka tsinci kansu, ya umarci dukkan hukumomin tsaro kada su huta har sai sun share baki ɗaya waɗan nan yan ta'addan."
"Dukkan hafsoshin tsaro suna nan, wanda hakan wata alama ce shugaban ƙasa na kokarin shawo kan wannan lamarin."
Yan bindiga na shigowa daga Zamfara - Tambuwal
Da yake nasa jawabin, Gwamna Tambuwal yace a kwanan nan yan bindiga da masu garkuwa sun jefa al'ummar Sokoto cikin mawuyacin hali.
A cewar gwamnan, luguden wutan dakarun soji na Operation Hadarin Daji a Sokoto don kawo karshen yan bindiga a Zamfara, shi ke koro su zuwa Sokoto.
Source: Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari