Wani magidanci mai sana'ar cacar Lotto ya banka wa kansa wuta ya mutu a jihar Osun.
Lamarin ya faru ne a Ikere na jihar Odun. Mai wajen cacar mai suna Seyi, ya kulle kansa a cikin shagonsa (Kiosk) kuma ya banka wuta.
Nan take wuta ta kama shagon lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
Wani ganau kuma makwabcinsa a wajen sana'a ya ce ana zargin cewa Seyi na fama da matsanancin damuwa sakamakon matsalar bashi.
Kakakin hukumar yansandan jihar Odun Yemisi Opalola ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce Yan sanda za su gudanar da bincike.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI