Malamin addinin musuluncin nan, Bello I. Yabo, ya shiga sahun masu sukar yunkurun gwamnatin Muhammadu Buhari na kara farashin mai.
A wani karatu da babban malamin ya yi a garin Sokoto a ‘yan kwanakin nan, ya bayyana cewa za su yi zanga-zanga, muddin litar fetur ta kai har N340.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa bidiyon wannan bayani da malamin ya yi a karatu ya fara bayyana ne a
Shehin yace idan har za a iya yin zanga-zanga a baya, saboda lita ta kai N65, to za a iya kare jini-biri jinni idan aka yi zanga-zanga don farashin ya kai N340.
Lallai kuwa idan aka kai litar man fetur N345, da mu za a fito ayi wannan zanga-zangar. Domin rainin wayon da rashin imanin ya yi yawa.”
“Idan har ana iya jagorantar zanga-zanga domin an kai lita 65, ina ganin idan an kai litar mai N345, lallai ya kamata ko kasha-kashe ayi.” - Bello Yabo.
Malamin addinin ya kara da cewa; Ayi zanga-zanga, kuma ya zama ‘bloody’, ma’ana ayi jina-jina.
Sheikh Bello Yabo ya yi alkawarin zai yi yi adawa da wannan matsaya, inda mabiyansa a masallacin suka tabbatar masa da cewa su ma su na bayansa.
Wannan malami da ya saba shiga gidan yari yace Allah ya sa ba a baki kurum mutane suke ta kurari ba, ta yadda za su janye su bar shi a ranar zanga-zangar. Ya sake tambayarsu
“Kun yi alkawarin idan an kai shi (N345) za ku fito” Mutane su ka ce kwarai.
Sai yace
“Duk wanda ya yi alkawari yace ‘Allahu Akbar’”. A nan ne masallaci ya dauka da kabarbarin Allahu Akbar kamar yadda aka ji a wannan bidiyon.
A karshe malamin ya yi murmushi, aka cigaba da kabarbara, ana yi masa addu’a, sai bidiyon ya kare.
Rikicin Bello Yabo da El-Rufai
A shekarun baya aka ji cewa Sheikh Bello Yabo ya shiga hannun jami'an tsaro tun bayan bazuwar bidiyon da ya caccaki gwamnan Kaduna a kan hana ayi sallar Idi.
A wani sautin murya mai tsayin kusan minti biyar, malamin addinin ya caccaki Gwamna Malam Nasir El-Rufai saboda ya hana sallar idi a dalilin annobar COVID-19
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari