Innalillahi: An tura yara zuwa Islamiyya, an tsinci gawarwakinsu a cikin wata mota


An tsinci gawarwakin wasu yara takwas a cikin wata mota da aka ajiye akan titin Adelayo, Jah-Micheal a Badagry ta jihar Legas. 

An ce yaran suna tsakanin shekaru hudu zuwa shida, inji rahoton TheCable. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 4 ga watan Disamba. 

Adekunle Ajisebutu, kakakin rundunar ‘yan sandan Legas, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi. 

Ajisebutu ya ce: "Yaran takwas an ce sun kulle kansu ne cikin wata motar da aka yasar a lokacin da suke wasa.

 “An gano gawarwakinsu kuma an ajiye su a dakin ajiyar gawa na babban asibitin Badagry domin a tantance ainihin musabbabin mutuwarsu." 

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma ce kwamishinan ‘yan sanda a Legas, Hakeem Odumosu, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan al’amuran da suka shafi mutuwarsu. Odumosu ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa. 

Da take bayyana yadda lamarin ya faru, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa, hudu daga cikin yaran ‘yan gida daya ne da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya.

 Wani mazaunin yankin mai suna Taiwo ya shaida cewa yaran sun je makarantar Arabiyya ranar Asabar da lokacin dawowarsu yayi kuma iyayensu ba su gan su ba sai hankali ya tashi, suka fara nema, inda aka gano gawarwakinsu daga baya.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN