A wani jawabi da ya yi wa manema labarai a wani faifen bidiyo, Kwamishinan yansandan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, ya shawarci masu motoci kirar Toyota kowane iri ne matukar mai tsada ce, har da Toyota Hilux, cewa su kula da motocinsu kwarai da gaske domin dai barayin mota sun fi mayar da hankali wajen satar motoci kirar Toyota.
Ya kuma shawarci masu motoci kirar Toyota su dinga amfani da na'urorin tsaro domin takura masu satar mota.
Ya ce an kama gungun wasu mutane da suka shahara wajen satar motoci su ketara da su zuwa jamhuriyar Nijar inda suke sayar da su ga wani dilar motocin sata.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka