Tsohon gwamnan Sokoto a arewacin Najeriya Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya bayyana takaicinsa kan kashe-kashen al'umma da 'yan bindiga ke yi a yankin, yana mai kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da "ya ji tsoron haɗuwarsa da Allah".
Tsohoin gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata hira da BBC Hausa kwanaki kaɗan bayan 'yan fashin daji sun ƙona wata motar bas ɗauke da mutum kusan mutum 30 a cikinta Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Sokoto.
Bafarawa ya ce: "Wajibi ne Buhari ya bi al'umma a zauna a tattauna kamar yadda ya bi su gida-gida lokacin da yake neman ƙuri'a, saboda mu taimaka masa wajen haɗuwarsa da Allah."
Hare-haren na masu garkuwa da mutane na ci gaba da haddasa salwantar rayukan al'umma a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya fi ƙamari a 'yan kwanakin nan a yankin Isa da Sabon Birni na jihar Sokoto da kuma yankin Shinkafi na jihar Zamfara duk da kokarin da gwamnatin tarraya da na jihohin ke cewa suna yi.
Latsa hoton da ke ƙasa ku saurari cikakkiyar hirar:
Video content
BBC Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka