Rahotanni daga jihar Sokoto na cewa jami'an tsaro sun fuskanci sansanin Yan bindiga daga yankin Buzai wasu kuma daga yankin Bafarawa cikin mota 14 tare da rakiyar jiragen yaki. An jiyo karar harbe harbe da manyan bindigogi ranar Juma'a 17 ga watan Disamba 2021. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Kazalika rahotun ya ce barayi Yan bindiga sun haye saman tsauni kimanin su 500, yayin da soji suka ja daga a wuri da ake kira Tusar biri, inda harbe-harbe ya ci gaba tsakanin Yan bindigan da sojin.
Babu cikakken rahotu kan adadin wadanda aka kashe daga bangaren soji ko na Yan bindiga.
Sai dai soji da masu taimaka masu sun ja daga a cikin dakin tare da Yan bindigan.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari