Tsohon shugaban jam'iyar APC reshen jihar Kebbi ya tona asirin dalili da ya sa aka cire shi, ya garzaya Kotu


Tsohon shugaban jam'iyyar APC na jihar Kebbi Arch. Bala Sani Kangiya, ya maka jam'iyyar APC a gaban babban Kotun tarayya da ke garin Birnin kebbi domin neman Kotu ta bi kadin hakkinsa na cire shi daga mukaminsa ba bisa kaida ba. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

A labaranta na ranar Juma'a 17 ga watan Disamba 2021, kafar labarai na Equity FM a Birnin kebbi ta labarta cewa Bala Sani Kangiwa ya shaida wa manema labarai cewa ya garzaya Kotu da ke Birnin kebbi domin neman Kotu ta tabbatar da tsarin doka dangane da fitar da shi da aka yi ba bisa ka'ida ba.

Ya ce kafin ya garzaya zuwa Kotu, ya bi dukkannin hanyoyin lumana a matakin jam'iyar na jiha da na kasa baki daya.

Alhaji Bala Sani Kangiwa ya ce an cire shi ne la'akari da karatowan zaben shugabannin jam'iyar APC duba da ba zai yarda a yi dauki dora ba shi ya sa suka cire shi ba bisa ka'ida ba.

Sai dai Kakakin jam'iyar APC na jihar Kebbi Isah Asalafi, ya ce shi kam baya da wannan labari

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN