Wani mazaunin Kano, Musbahu Rabiu Gyadi-Gyadi, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa yan daban da suka kai harin sun kai mutum 500.
Wannan na zuwa ne kwana kaÉ—an bayan kotu ta rushe shugabannin APC na bangaren gwamna Ganduje na jihar Kano, sannan tabbatar da bangaren Malam Shekarau.
Yadda lamarin ya faru Rahoto ya nuna cewa É—aruruwan yan daba sun kai harin ofishin wanda ke kan hanyar Maiduguri da yammacin ranar Laraba.
Ginin da abun ya shafa mallakin tsohon ministan kwadugo ne, Alhaji Musa Gwadabe. A halin yanzun jami'an yan sandan jihar Kano sun mamaye sakateriyar APC ta tsagin Shekarau, domin shawo kan lamarin.
Da muka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace yana cikin taro ne a lokacin.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku abinda wasu yan siyasa a jihar Kano ke cewa dangane da wannan lamarin. Wani É—alibi a jami'ar BUK, kuma mai bibiyar al'amuran siyasa É—an asalin jihar Kano, Honorabul Hafeez Kiido, yace:
"Yanzu tsarin siyasar da ake kira kyan-kyasar siyasa shine wannan? Ashe haka demokaraÉ—iyyar take? Kawai dan wasu sun É—auki layi daban da gwamnati a siyasance, sai a kone musu waje a nemi cutar da su kuma abun kunya da yan daba."
"Akwai takaici sosai tsarin siyasar Kano, tabbas babu kwayar zarra ta ilimi a wannan aiki. Kuma wannan ƙara bude kofar dawo da siyasar daba ce irin ta 2003-2007 a Kano."
Legit Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI