Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya magantu kan bukatarsa na sasantawa da abokin hamayyarsa, tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso da tsagin APC karkashin shugabancin Sanata Ibrahim Shekarau.
A sakon sabuwar shekara, wanda kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba yasa hannu a ranar Juma'a, Ganduje ya ce zai sadaukar da sabuwar shekarar wurin tabbatar da sabon tsarin zaman lafiya da sasanci tsakanin masu ruwa da tsakin jam'iyyun siyasa a jihar da kasar baki daya, Daily Nigerian ta ruwaito.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, duk da gwamnan bai kira sunayen 'yan siyasan ba, takardar ta jaddada bukatar shugabannin kungiyoyin siyasa na jihar da su hada kai domin kawo sabon tsari a siyasar jihar.
Ya ce:
"A yayin da aka ga manyan 'yan siyasar Kano suna jaddada bukatar sasanci, hakan ya sa jama'ar Kano fadawa farin ciki wadanda suke bukatar zaman lafiya da sasanci domin hakan ya kawo cigaba a siyasa da al'umma baki daya."
A cikin takardar, an tattauna kan yadda rashin tsaro ya tsananta a fadin kasar nan da kuma yadda talauci ya samu wurin zama a kasar nan.
Ya bayyana cewa, akwai tabbacin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na kokari wurin shawo kan matsalolin da suka addabi kasar nan.
Labari
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI