Da duminsa: Allah ya tona asirin wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a jihar Niger, duba ka gani


Rundunar 'yan sandan jihar Niger, ta yi ram da matashi mai shekaru 26 mai suna Umar Mohammed wanda aka fi sani da Babuga Yellow, kan zargin garkuwa da mutane, Punch ta ruwaito. 

A wata takarda da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, yasa hannu a ranar Juma'a a Minna, wanda ake zargin ya bayyana cewa tawagarsa ta shirya aikata mummunan aiki kafin a kama shi. 

Ya bayyana cewa, miyagun sun shirya sace wasu fitattun mutane biyu a kauyen Garatu," takardar tace. 

Punch ta ruwaito cewa, wanda ake zargin ya kara da bayyana sunayen abokan aikinsa wadanda har yanzu ba a kama su ba, inda ya kara da cewa suna da hannu wurin garkuwa da mutane tare da karbar kudin fansa da kuma satar shanu. 

A yayin tuhuma, ya sanar da cewa ya na cikin kungiyar 'yan bindiga wadanda suka kware da satar shanu tare da satar mutane domin karbar kudin fansa. Ya bayyana sunanyen 'yan kungiyarsu kamar haka: Bokolore, Ruwance, da Giware wadanda yanzu haka basu shigo hannu ba. 

Bayan jerin bincike, ya bayyana cewa sun dinga satar shanu a wurare daban-daban da suka hada da Beji, Wushishi da Kataeregi," Wasiu yace. 

Wasiu ya ce 'yan sanda sun yi ram da wani Musa Yakubu mai shekaru ashirin dauke da bindigar toka babu harsasai, inda ya kara da cewa a yayin tuhumarsa da aka yi, ya yi ikirarin cewa ya siya bindigar daga wani wanda bai san sunansa ba amma ya na zama a kauyensu. 

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN