Cikin Hotuna: Abin da yan daba suka yi a wajen taron siyasar PDP a Zamfara, duba yadda ta faru


Awanni kaɗan kafin fara taron jam'iyyar PDP reshen Zamfara, wasu yan daban siyasa sun farmaki filin da aka shirya gudanar da taron. 

Da farko PDP ta shirya gudanar da taron a Zaitun Oil mill dake bayan ofishin hukumar alhazai na jihar, amma daga baya aka maida shi Command Guest House Gusau. 

Wani mamban jam'iyyar PDP, Muhammad Mudassir, ya rubuta a shafin Facebook, cewa yan daban ɗauke da makamai sun yi mummunan ta'adi a wurin. 

Sakatare na musamman ga mataimakin gwamnan jihar, Umar Aminu, yace lamarin ba zai tsorata jam'iyyar PDP ba, kuma taron zai gudana kamar yadda aka tsara. 

Yace har yanzun babu wanda yasan su waye suka kai harin, amma ya bada tabbacin cewa hukumomin tsaro za su gudanar da bincike. 

Har yanzu babu tabbacin wace jam'iyyar siyasa ke da alhakin kai hari ga wurin taron jam'iyyar PDP na jihar Zamfara ba. 

Duk da kai harin, mataimakin gwamna, Barista Mahdi Aliyu Gusau, da shugaban PDP na riko, Ambasada Bala Mande, sun dira filin taron. 

Legit
Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN